BUDADDIYAR WASIKA ZUWA GA USTAZ ABUBAKAR SHEKAU

Daga Yasir Ramadan Gwale

Dukkan irin dangin yabo da godiya da kirari sun tabbata ga Allah madaukakin sarki, tsiranSa da AmincinSa su kara tabbata ga fiyayyan halitta Manzon tsira Annabi Muhammad Salallahu Alaihi Wasallam da alayansa da sahabbansa da kuma wadan da suka bi tafarkinsu har ya zuwa ranar sakamako. Ina shaidawa babu abin bautawa bisa cancanta sai Allah kuma Annabi Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa ne. Ina bude wannan wasika da mafificin kalami, shine, Assalamu Alaikum Warahmatullahi Wabarakatuh.

Ustaz Abubakar Shekau, na zabi rubuta maka wannan wasika ne, domin isar da wani sako a gareka, dan tunasar da kai abubuwan da ka sani, Manzon Allah yace Ku tunasar domin tunasarwa tana amfanar Munumai (Hadith). Ina fatan wannan sako na wa zai isa zuwa gareka cikin Aminci. Muna rokon Allah ya Amintar da mu a dukkan inda muke.

Uztaz Shekau, da farko ina mai yin kira a gareka da kaji tsoron Allah! Ka sani cewa dukkaninmu a wannan duniya, ba komai muke ba face bayi masu bauta ga Ubangijinmu mahalicci, kamar yadda ya fada a cikin littafinSa mai tsarki a cikin sura ta 51 aya ta 56 cewa ban halicci dan-Adam da al-jani ba face dan su kasance masu bauta a gareni, Subhanahu wata’ala, tsarki ya tabbata a gareshi! Allah Subhanahu Wata’ala ya aiko mana da Manzo wanda shine cikamakin Annabawa dan ya zo ya sanar da mu Addini, kamar yadda ya fada, lallai addini a wajen Allah shine Muslunci/ Islama. Alhamdulil Lah, muna yiwa Allah godiya bisa wannan ni’ima ta kasancewarmu Musulmi ba dan zabinmu ba, sai dan haka ya hukunta. Alhamdulillah!

Haka kuma, Allah madaukakin sarki ya fada a cikin sura ta 76 aya ta 2 cewa Hakika mun halicci mutum daga digon maniyyi gaurayayye don mu jarraba shi. Kuma muka sanya shi mai ji da gani. Wannan aya ta nuna mana cewa shi mutum dan adam ba komai yake ba a wajen Allah, domin Asalinsa wani ruwa ne gaurayayye kamar yadda Allah ya fada, wato dukkan wani mahaluki a bankasa Maniyyi ne me wari. Dan haka babu abin da ya dace dan Adam ya shagalta da shi face neman dacewa a wajen ubangijinSa mahalicci. Ya Allah muna rokonka tare da tawassuli da kyawawan sunayanka madaukaka ka sa mu dace da rahamarka kuma ka tseratar da mu daga Azabarka.

Uztaz Shekau, ina zaton kana sane da irin halin da al’ummar kasar Arewa suke ciki a Najeriya na zullumi da tsoro da firgici da tashin hankali da razana da rashin kwanciyar hankali. Uwa uba kuma ga tsananin talauci da fatara da ya yi mana katutu, kuma yake karuwa a wannan lokaci, da yawan mutane suna cikin wannan firgici ne akan abinda basu san hawa ba kuma basu san sauka ba. Hakika Allah madaukakin Sarki ya fada a cikin Al-qur’ani, sura ta 29 aya ta 2 cewa, Shin mutane suna zaton za a kyale su haka nan don sun ce “Mun yi imani” ba tare da an jarrabe su ba. Hakika sai an jarrabi mutane da tsanani da tashin hankali! Ya Allah muna rokonka kada ka jarrabemu da abinda bazamu iya jurewa ba. Ustaz Shekau, ina kira a gareka cewa kaji tsoron Allah ka yi kira ga mutananka akan ku ajjiye makamai ku kyale al’umma su samu walwala, a bisa wannan tsanani da muke ciki, musamman irin yadda al’umma suke ta kiraye-kirayen neman zaman lafiya da yin addu’o’i.

Haka kuma, Kamar yadda muka samu labari cewa asalin abin da ya fusata ku, ya sanya kuka dauki (doka a hannu) makamai shine kashe muku mutane da aka yi a yayin da kuke hanzarin zuwa jana’izarsu a garin Maiduguri a shekarar 2009. A bisa yadda muka ji ana ruwaito ku kuna fada cewa wannan yana daga cikin dalilin da ya sanya kuka dauki doka a hannunku! Uztaz Shekau shin yanzu baza ku yi duba ya zuwa wannan ayar da ke cikin suratu ankabutu ba, ku maida lamuranku ga Allah, domin Allah yace sai an jarrabemu? Shin abinda ya sameku ba jarawabawr Ubangiji bace? Shin bazaku kasance masu da’a a gareshi ba Subhanahu wata’ala? Shin ko kun manta fadin Allah madaukakin sarki a cikin Sura ta 3 aya ta 142 cewa, Shin ko kuna zaton za ku shiga Aljanna ba tare da Allah ya san wadanda suka yi kokari daga cikinku da kuma wadanda suka yi hakuri (juriya) ba? Shin kun manta da wannan ayar ne, Shin bazaku kasance daya daga cikin mutanan da Allah yake buga misali da su ba cikin masu hakuri da juriya ba?

Haba jama’a! ku sani biyayya ga shugabanni wajibi ne a cikin addinin Musulunci. Daukar doka a hannu wannan ya sabawa koyarwar addinin Musulunci. Lallai kuji tsoron Allah ku ajjiye makamai ku karbi wannan ahuwa da manyan mutane suke ta kira ga hukuma akan tayi muku. Sahabin Manzon Allah mai daraja Khalid Ibnu Waleed Allah ya kara yarda da shi, a lokacin da aka je yaki dan yin jihadi, ya daga takobi zai sare kan wani Mushriki sai ya furta kalmar shahada amma duk da haka Khaled ya fille kan sa, daga baya ya baiwa Manzon Allah labarin abinda ya aikata, nan take Manzon Allah yace “Allumma inni abra’u ilayya min ma san’a kahiludn” Manzan Allah ya barranta daga abinda khalid ya aikata na kashe mutumin da ko sallah bai taba yi ba, kawai furta kalmar Shahada ya yi! Shin tsakaninku da Allah zaku iya kididdige adadin yawan mutanan da suka rasa rayukansu ta sanadiyar abubuwan da hannayanku suka aikata, a jihohin Borno da Yobe da Bauchi da Kano da sauran jihohi? Shin bakwa jin tsoron Azabar Allah ne? Lallai dukkanmu Musulmi munyi Imani da cewar Allah mai tsananin Ukuba/Azaba ne! Kuma ku sani tun daga farkon duniya har karshenta Allah bai halicci wata RAI da zata iya jurewa azabarSa ba, Hasbinallahu wani’imal wakeel! Shin kuna tunanin azabar Allah kuwa? Lallai idan kun manta ku fadaku cewa Allah mai tsananin azaba ne ga wadan da suka aikata laifuka.

Mutane newa ne suka tagayyara a wadannan jihohi ta sanadiyarku? Mutum nawa kuke zaton kun halaka da basu san hawa ba, kuma basu san sauka ba? Ku kun kashe sannan jami’an tsaro suma sun kashe. Tsammaninku ko da anyi muku ahuwa kun karba shike nan shima Allah ya yi muku ahuwa? Bakwa tunanin makomarku? Bakwa tunanin irin mutanan da suka rasu ta sanadiyarku? Wallahi ku sani rayuwar duniya ba komai bace sai wargi kamar yadda Allah ya fada a cikin sura ta 29 aya ta 64 cewa Rayuwar duniya ba komai ba ce sai wasa da wargi. Lahira – wannan ita ce rayuwa ta hakika, in da sun san haka. Lallai ku kasance masu tuna lahira da tunanin makomarku idan an koma lahira! Lallai ku sani Lahira gaskiya ce, Wuta gaskiya ce, Al-jannahma gaskiya ce. Tabbas, wadan da suka cancanci shiga wuta babu makawa sai sun shigeta komai dadewar da suka yi a duniya. Haka kuma Allah yana fada a cikin sura ta 35 aya ta 5 cewa Ya ku mutane! Alkawarin Allah gaskiya ne. Kada rayuwar duniya ta rude ku kuma kar mai rudi ya rude ku a cikin al’amarin (bin) Allah, lallai kuyi duba na hankali zuwa ga wadannan ayoyi idan kun kasance Musulmi na gari masu Imani.

Dan haka, ku sani tunda Allah ya halicci duniya babu wanda ya taba kaucewa mutuwa, babu kuma mai iya kauce mata. Allah ne ya fada a acikin littafinsa mai tsarki cewa kowacce RAI sai ta dandana mutuwa. Dan haka Lallai ne, Uztaz Shekau ka tunasar da mutananka cewa Alkawarin Allah gaskiya ne, kuma baya tashi. Mutane da yawa sun shiga cikin firgici da damuwa da tashin hankali duk a sanadiyarku, lallai kuji tsoron Allah ku bar mutane su sakata su wala a cikin garuruwansu, kamar yadda sauran al’ummatai na gurare daban daban suke watayawa a cikin kasashe da garuruwansu.

Shin bazaku yi kokari ku zama daga cikin mutanan da Allah yake buga Misali da su a cikin Suratul Bakara ba inda yace suna neman Sabati a duniya da lahira, kamar yadda ya ce a aya ta 201 “Daga cikinsu kuma akwai masu cewa ‘Ya Ubangijinmu, ka ba mu kyakkyawa a duniya da kuma kyakkyawa a lahira, kuma ka tsare mu daga azabar wuta.” Shin bazaku kasance cikin wadannan mutane da Allah ya bada labarinsu ba? Haka kuma, Allah yana fada a cikin sura ta 70 aya ta 60 cewa Masu kyautatawa basu da wani sakamako a wajen Allah face kyautatawa, kamar misalin haka ne ga duk wadan da suka munana ko suka tsanantawa Al’ummar Manzon Allah, Allah zai tsananta musu ya munana musu, Allah ya kiyashemu.

Lallai ku sani Manzon Allah yace dukkan mutumin da wani ya dauki wani nau’i daga cikin nau’ukan makamin da zai iya yin kisa ya kashe mutumin da bai jiba ba kuma gani ba, lallai ranar lahira wanda aka kashe din zai kamo wuyan wanda ya kashe shi zuwa gaban Allah, yace ya ubangiji tambayi wane me nayi masa ya kasheni! Shin mutum nawa kuke zaton zasu kamo wuyanku a ranar Alkiyama dan neman fansar jininsu da kuka yi sanadiyar kwararsa ba tare da hakki ba? Lallai kuji tsoron firgici da razani da yake tattare da ranar tashin alkiyama, ranar da kudi da mulki da zurriyya da sanayya baza ta amfanawa da kowa komai ba, sai kawai wanda ya zowa da Ubangiji da tsarkakkiyar zuciya.

Daga Karshe, Uztaz Abubakar Shekau, Ina kara jadda magana ta a gareka da kaji tsoron Allah kaida jama’arka! Kuma ku sani a tare da dukkaninmu akwai mala’iku masu kididdige aikin kowannemu. Duk wanda yayi alkhairi komai kankantarsa zai gani, haka duk wanda yayi kishiyarsa komai kankantarsa shima zai gani. Wasu zasu zo suna cewa wannan wanne irin littafi ne da bai bar komai ba. Wasu kuwa suna cewa “Ha’u muqra’u kitabiya” Ku sani ku kara sakankancewa Babu wani mahaluki da zai iya jure azabar Allah, kuma Allah da kansa ya kore zalunci akan kansa, sannan ya ce sai ya sakawa duk wanda aka zalunta yayi Allah ya isa ko bai yiba. Sai dai fa idan wanda aka zalunta din ne yace ya yafe, shin mutanan da kuka zalunta a ina zaku gansu ku iya neman gafararsu? Idan wadan da suke raye sun yafe, wadan da suka rigamu gidan gaskiya kuma fa? Allah shine shaheed!

Ya Allah muna rokonka ka Amintar da mu a cikin garuruwanmu, Ya Allah ka bamu zaman lafiya mai dorewa, Ya Allah duk mai neman shiriya daga cikinmu Allah ka shiryeshi kayi masa jagora, wanda kuma baya nemanta ya kangare mata, Ya Allah ka tozarta shi ka wulakanta shi, ka nesanta al’ummar Manzon Allah daga kaidi da makircinsa. Ya Allah mun tuba ka karbi tubanmu.

Yasir Ramadan Gwale
20-04-2013″

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s

%d bloggers like this: