Ana so iyaye su rika yiwa ‘ya’yansu addu’ar nan akai-akai ko da yaushe.

Ya Allah Ka yiwa ‘ya’yana albarka, Ka sa su zama masu yima Ka biyayya, Ka azurtasu da yi min biyayya, Ka sanar dasu ilimi kamar yadda ka sanar da Annabi Musa, Ka basu fahimta kamar yadda Ka fahimtar da Annabi Sulayman, Ka basu hikima da iya zance kamar yadda Ka baiwa bawanKa Lukman, Ka basu ilimin abinda basu sani ba, Ka tunasar dasu abinda suka manta, Ka bude musu albarkar sammai da kassai, Allah Kai Mai ji ne kuma mai amsawa. Allah Ka bawa ‘ya’yana kaifin hadda, Ka basu saurin ganewa, Ka basu tsarkin tunani, Ka sa su zama shiryayyu masu shiryarwa, Ka saukar da imani a cikin zukatansu, Ka k’awata zukatan su da imani, Ka sa masu kyamar kafirci ne da fasikanci da kuma sabo, Ka sa su cikin shiryayyu, Ka gyara halayensu, Ka cika zukatansu da haske da hikima, Ka tsarkake zukatansu da barin riya, Ka tsarkake gaban su, Ka kare su daga zina, luwadi, madigo da dukkan laifuffuka, Allah ka tsare min zurriyata.

Ya Allah Ka sa su zama mahaddatan Qur’ani, su zama masana ga sunnar Annabin Ka Muhammad SAW, Ka azurtasu da kamewa da kuma yarda da hukunci da Ka yi a kansu, Ka azurtasu da kaunar Ka da kaunar AnnabinKa da kaunar wanda Kake kauna da kaunar duk wani aiki da zai kusantar dasu da samun soyayyarKa, Ka bude musu kofar arziki na halal daga mayalwaciyar falalarKa kuma Ka wadatar dasu halal da barin haram, Ka nisantar dasu daga abokai ko kawaye munana da zasu bata tarbiyar su ko halayensu Ka raba su da alfasha da dukkan mummunan abu.

Ya Allah Ka sa su zama masu lafiya a jikinsu, Ka kare kunnuwan su, idanuwan su, rayukansu da kuma gabobinsu daga sabon Ka Ya Mai jin kan masu jin kai.

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s

%d bloggers like this: