Ga Sakon Malam Sa’adu Zungur Na Waka Sama Da Shekara 50 Amma Kamar Yau Ya Gabatar

“Matukar a arewa da karuwai,
yan daudu dasu da magajiya.

Da samari masu ruwan kudi,
Ga mashaya can a gidan giya.

Matukar yayan mu suna bara,
Titi da Loko-lokon Nijeriya.

Hanyar birni da na kauyuka,
Allah baku mu samu abin miya.

Sun yafu da fatar bunsuru,
Babu mai tanyonsu da dukiya.

Babu shakka yan kudu zasu hau,
Dokin mulkin Nijeriya.

In ko yan kudu sunka hau,
Babu sauran dadi, dada kowa zai sha wuya.

A Arewa zumunta ta mutu,
Sai karya sai sharholiya.

Camfe-camfe da tsibbace tsibbacen,
Malaman karya yan damfara.

Sai karya sai kwambon tsiya,
Sai hula mai annakiya.

Ga gorin asali da na dukiya,
Sai kace dan annabi fariya.

Jahilci ya ci lakar mu duk,
Ya sa mana sarka har wuya.

Ya sa mana ankwa hannuwa,
Ya daure kafarmu da tsarkiya.

Bakunan mu ya sa takunkumi,
Ba zalaka sai sharholiya.

Wagga al’umma mai zata yo,
A cikin zarafofin duniya.

Kai Bahaushe ba shi da zuciya ,
Zaya sha kunya nan duniya “.

“Mu dai hakkin mu gaya muku,
Ko ku karba ko kuyi dariya.

Dariyar ku ta zam kuka gaba,
da nadamar mai kin gaskiya.

Gaskiya ba ta neman ado,
ko na zakin muryar zabiya.

Karya ce mai launi bakwai,
ga fari da baki ga rawaya.

Ga kore ga kuma algashi,
toka-toka da ja sun garwaya”.

Advertisements

3 Comments (+add yours?)

 1. mohammed auwal
  Mar 07, 2013 @ 05:13:06

  Sincerly yours,
  The text that i was oppurtuned to read today from my learnerd friend, reminds me of my secondary school days in the late seventies.
  It is of the fact what the northern nigeria is wittnessing today.
  In hausa language there is an adage which says:a bin da babba ya hango yaro,ko ya hau
  tsauni mai tsawo bashi hangowa.

  This was the vision of visioner of which time con tranlate

  Reply

 2. YAHAYA ABUBAKAR KARFI
  Mar 08, 2013 @ 17:35:45

  Allahu Akbar,Wallahi yayi gaskiya gashi yanzu muna gani! Allah ka ganar da mutanen mu na arewa.Halima Allah ya saka maki da Alheri.

  Reply

 3. Aliyu Paiko
  Mar 09, 2013 @ 10:41:30

  Nothing can be truer than this, abin da “Tirrr-assha”!!

  Reply

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s

%d bloggers like this: