MU TASHI MU FARKA AFIRKAWA

Map of Africa

Kira na ke Afirkawa
Gare mu kira Afirkawa
Ba don na fi ku komi ba
Duk mu zo mu yo gyara
Zamani ya bar mu can baya
Me za mu barwa ‘yan baya
Mu daina yakin kisan juna
Daga Kwango zuwa Somalawa
Ivory Coast da Libiyawa
Sudan,Darfur da Jubawa
Fadin nahiyar Afirkawa
Mu zo mu zauna mu so juna
Mu fasa fadan kashe juna
Mu tashi mu,ma kamar kowa
Yawan jama’a kar ya zam banza
Al’adun mu har da su,su ma
Ma’adinai duk akwai a kasa
Aiki ke gina kasar kowa
Ba barcin da ba iyaka ba
Ba yawan fada da juna ba
Ba taimakon kasashen ba
Yalwar kasa Jallah Ya bayar
Hikima, Ya ba Afirkawa
Mu farka mu bar kwana
China mu barwa Sinawa
Rasha mu barwa Rashawa
Turai mu barwa Turawa
Amurka ko ga Amurkawa
Afirka ta mu,mu Afirkawa

Posted with WordPress for BlackBerry.

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

w

Connecting to %s

%d bloggers like this: