RANAR ZABE NA ZUWA

Stolen Election in 2008?

Image by Sokwanele - Zimbabwe via Flickr

Rayuwar mu ta wannan zamani
Babu dadi sai tarin wuya
Wahalhalu,kullum jiya gara yau
Magidanta na ta kururuwa
samari na zaman kashe wanduna
Babu aiki babu wurin zuwa
Masana sun kammala Jami’a
Ba su aiki sai yawon bara
Masu aikin ba su ganin biya
Shugabanni ko ba su damu ba
Ba ruwan su da k’uncin rayuwa
Wahala ko kad’an ba su san ta ba
Dukiya ta k’asa sun wawashe
Arzikin kowa sun handame
Sun tattare sun kai ajiya waje
Su kadai ke cinye kudin k’asa
Sun yi tumbi ga k’aton wuya
Mutum d’aya!motoci tara!
Ba su yunwa, ba su k’ishin ruwa
Aikin Haji, ya zama ma riya
Talakawa na ta bagauniya
Su na neman lauma d’aya
Sara suka shi za su yi
Kalare gami da jagaliya
Don su samu abun tsotson k’ashi
Makarantu babu abun zama
In akwai ma, babu rufin sama
Abun rubutu, shi ma babu shi
Asibitoci gara kufai da su
Magani ba k’waya ko d’aya
Ba ruwa, ba hanya, ba tsaro
Ba wuta, ba takin zamani
Ba adalci, ba gaskiya
Ba shari’a, ba a tausayi
Nan kusa zabe na zuwa
Kar mu yarda a kai mu gidan jiya
Mu fito ran zabe mu duka
Ran nan dafifi za mu yi
Mu yo fitar tururuwa
Babu tsoro, ba wata fargaba
Mu yi zabin sauyin rayuwa
Jallah Sarki Kai ma na taimako
Jabbaru Kai ma na Jagaba
Ka taya mu a zabin shugaba
Kar ka bar mu,mu zaba mu kadai
Taimake mu a zaben shugaba
Ya Salam kare mu gaba daya
Mu yi zabe babu hayaniya.

  Advertisements

  3 Comments (+add yours?)

  1. YAHAYA ABUBAKAR KARFI
   Mar 21, 2011 @ 00:14:09

   Gaskiya allah ya baki kwakwalwa halima,Allah ya karama maki basira amen.

   Reply

  2. Abdullahi yusif
   Mar 21, 2011 @ 12:04:22

   Allah ya taimakeki dawannan sadaukad da kai da kikeyi,amin,mun gude maki Halima.

   Reply

  3. Hussein suleiman A
   Mar 22, 2011 @ 16:17:52

   Aunty wannan gargadi yayi kyau. Allah sa mu gane. Allah kara maki basira da hazaka.

   Reply

  Leave a Reply

  Fill in your details below or click an icon to log in:

  WordPress.com Logo

  You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

  Google+ photo

  You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

  Twitter picture

  You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

  Facebook photo

  You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

  w

  Connecting to %s

  %d bloggers like this: